1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane a Afganistan

Binta Aliyu Zurmi
March 6, 2020

Wasu 'yan bindiga sun halaka a kalla mutane 27 yayin da wasu 29 suka jikkata a wani hari da aka kai kan masu zaman jimamin tunawa da mutuwar wani jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Kabul babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3Yyca
Afghanistan Kabul Polizei erscheint nach Schießerei
Hoto: AFP

Wannan biki na cika shekaru 25 da mutuwar Abdul Ali Mazari, da ke zama shugaban 'yan kabilar Hazaras da mafi yawansu 'yan Shi'a ne, ya gudana ne a yau Juma'a, wanda ake zargin mayakan Taliban da kai musu hari, ganin yadda a baya suka sha kai ma 'yan Shia'ar hari.

Mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar kasar, Wahidullah Mayar ya tabatar da aukuwar wannan lamari, inda ya kuma kara da cewar tuni aka kai wadanda suka jikkata asibiti. 

A hannu guda kuma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida Nusrat Rahimi ya ce an jima ana ta dauki ba dadi tsakanin yan bindigan da jami'an tsaro, lamarin da ya kara tsorata jama'a wanda ya sa mutane guduwa don tsira da rayukansu.