1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe mutane 12 a Kwango

Mouhamadou Awal Balarabe
June 9, 2023

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin na yankin Bukokoma na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, amma ana danganta shi da irin wanda kungiyar ADF da ke da alaka da IS ta saba kaiwa.

https://p.dw.com/p/4SNiM
Garin Beni na Kwango ya yi kaurin suna a fannin rikice-rikiceHoto: Alexis Huguet/AFP/Getty Images

Wasu da ake zargin mayakan da ke da kaifin kishin Islama ne sun kashe mutane 12, a wani harin da aka kai a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da ke fama da rikici. Wani jami'in gudanarwa a yankin Bukokoma ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, ‘yan bindigan sun yi amfani da adduna wajen fille kawunan wadanda da aka kai wa harin. Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin wannan ta'asar, amma dai ana dangantata da kungiyar ADF da ke da alaka da IS.

Wannan harin ya biyo bayan wani rikici da ya barke a yankin Beni a makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara. Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ta bayyana cewar sama da mutane 50 ne aka kashe a yankin Beni a watan Mayu kadai. Hare-hare na ci gaba da wakana a gabashin Kwango duk da farmakin hadin gwiwa da sojojin Kwango da na Yuganda suke kai wa kan mayakan ADF tun shekaru biyun da suka gabata.