′Yan bindiga sun kai hari ofishin ′yan sandan Najeriya | Labarai | DW | 26.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sandan Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan ofishin 'yan sanda da ke Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan ofishin 'yan sanda da ke Abuja fadar gwamnatin Najeriya, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.

'Yan sandan sun mayar da wuta lokacin da maharan su ka yi yunkurin kubutar da wadanda ake tsare da su, a helkwatar rindunar mai kula da miyagun laifuka. Babu rahoto game da wadanda harin ya shafa. Kuma tuni 'yan sanda sun kaddamar da bin sawun maharan.

Wannan ya faru sa'a'i bayan harin kunar bakin wake kan wata majami'a a garin Kaduna na arewacin kasar, ya yi sanadiyar hallaka mutane 11, tare da jikata wasu kusan 30. Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin duk hare hare, amma ana dangantawa da kungiyar Boko Haram mai dauke da makamai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasir Awal