′Yan bindiga sun kai hari caji ofis | Labarai | DW | 21.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kai hari caji ofis

A Afrika ta Kudu, wasu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyar da soja daya a wani hari da suka kai caji ofishin 'yan sanda da ke a yankin birnin Cape Town a safiyar wannan Laraba.

A wata sanarwar da mahukunta suka fitar jim kadan da kai harin, sun ce 'yan bindigan sun kwashi wasu makamai daga ofishin kafin su tsere a cikin wata motar 'yan sanda da suka sace daga harabar ofishin.

Kakakin 'yan sanda yankin Khaya Tonjeni ya fadi cewa ana kan gudanar da bincike don gano wadanda suka kai harin, ya kara da cewa za'a gano su duk inda suke aka kuma hukunta su kan wannan kisan da suka aikata. Gwamnatin kasar ta baiyana takaici tare da kwatanta ranar a matsayin rana ta bakin ciki ga al'ummar Afrika ta Kudu.