1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun harbi Firaministan Slovakia

Abdul-raheem Hassan
May 15, 2024

Wasu 'yan bindiga dadi sun harbi Firaministan kasar Robert Fico, rahotanni sun ce an harbe Mr. Fico ne jim kadan bayan kammala wani taron majalisar ministoci a birnin Handlova da ke tsakiyar kasar.

https://p.dw.com/p/4ftQv
Firaiministan Slovakia, Robert FicoHoto: Petr David Josek/AP Photo/picture alliance

Jaridar Dennik N daily, wacce wakilinta ya ga yadda jami'an tsaro suka dauke firayim minista a cikin mota, ya ruwaito cewa ‘yan sanda sun tsare dan bindigar da ake zargi, kuma tuni aka garzaya da shi asibiti.

A martaninta na farko game da harbin, Shugabar gwamnatin Slovakia mai barin gado Zuzana Caputova ta bayyana kaduwarta matuka da harin da ta kwatanta da "rashin tausayi".

Mista Fico ya koma kan karagar mulki a Slovakia bayan zabe a watan Satumban shekarar 2024, a karkashin wani kawancen masu ra'ayin kishin kasa.