′Yan bindiga sun hallaka mutane da dama a Amirka | Labarai | DW | 03.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun hallaka mutane da dama a Amirka

Wasu mutane dauke da makammai sun buda wuta a ranar Laraba a birnin San Bernardino da ke jihar Californiya ta kasar Amirka, inda suka hallaka mutane 14.

Bayan hallaka mutane 14, maharan sun kuma jikkata wasu mutanen 17 a cewar hukumomin yankin. 'Yan awoyi bayan wannan hari ne dai jami'an tsaro na 'yan sanda suka harbe biyu daga cikin maharan da suka hada da wani namiji da mace. Sai dai kuma jami'an tsaron sun kame wani mutun na uku da ke kokarin tserewa cikin wata mota, amma kuma sun ce babu tabbacin ko yana daga cikin masu kai harin a cewar Jarrod Burguan shugaban 'yan sandan birnin na San Bernardino yankin da ke a nisan km sama da 100 da birnin Los Angeles.

Mai yuyuwa ne dai daya daga cikin mutanen uku da suka kai harin ya gudu, kuma ana zaton cewa akwai wadanda suka taimaka a ka kai wannan hari. Tuni dai shugaban kasar ta Amirka Barack Obama ya yi Allah wadai da hari inda masu bincike ke ci gaba da ayyukansu kan lamarin.