′Yan Afirka ta Kudu na neman Zuma ya sauka | Siyasa | DW | 07.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan Afirka ta Kudu na neman Zuma ya sauka

Dubban masu zanga-zangar lumana sun yi jerin gwano a manyan biranen kasar Afirka ta Kudu domin kira ga shugaba Jacob Zuma da ya yi murabus bayan da bashin da ake bin kasar ya tsananta.

Masu gangamin sun fara jerin gwano ne daga biranen Johannesburgh da Pretoria da Cape Town da wasu manyan garuruwa, a wani mataki na tilasta wa shugaba Zuma ya sauka daga kujerar mulki, kan abun da suka bayyana da rashin cancanta. Matakin sallamar ministan kudin kasar cikin garambawul da shugaba Zuma ya yi a ranar Alhamis na makon jiya, ya tayar da jijiyoyin wuya a kasar, ciki kuwa har da 'ya'yan jam'iyyar ANC mai mulki tun cikin shekara ta 1994 bayan mulkin fararen fatan kasar.

Wannan mataki na shugaban kasar dai a cewar manazarta na barazanar karuwar ayyukan rashawa da kara durkusar da tattalin arzikin kasar. Jam'iyyar adawa mafi girma ta Demokratic Alliance ce ta shirya wannan gangami na adawa. Anne-Marie van de Lindelm na daga cikin masu gangamin, inda ta ce " Na zo nan domin nuna goyon baya ga kasata, domin gyara makomarta , a maimakon ci gaba da zama a karkashin mutum guda da yayi babakere akan komai".

Koran tsohon ministan kudi Gordhan ne ya janyo suka ga Zuma a bangaren 'yan Afirka ta Kudun da ma masu zuba jari na kasa da kasa, wadanda ke ganin ministan da kima, kamar yadda Dorion Koma  da ke wannan gangami ya nunar

Südafrika Proteste gegen Präsident Zuma (Reuters/M. Hutchings)

Jerin gwanon ya samu karbuwa a birane da dama

. Ya ce " ANC jam'iyya ce mai son azurta kanta, duk wadanda ke gwamnati na kokarin azurta kansu, dalili kenan muke yakar wannan azurta kan".

Masu gangamin na dauke da kwalaye da aka rubuta " Ceton Afirka ta Kudu daga Zuma da Gupta". 'Yan jam'iyar ANC mai mulkin cikin kayan sarki ne dai suka yi wa ginin headquatar jam'iyyar kawanya domin kare masu zanga-zangar da ke shigewa ta wurin daga shiga. Mabel Rweqana 'yar jam'iyyar ANC ta ce " Irin wannan gangami ya kan rikide daga lumana zuwa jefan motoci da gine-gine, har da dibar ganima. Don haka mun zo ne domin tabbatar da cewar hakan bai auku da wannan ginin ba".

Gwamnatin Afirka ta Kudun ta bukaci gudanar da gangamin cikin lumana, tare da jaddada cewar tana daraja 'yancin al'ummar kasar na gudanar zanga-zanga, kamar yadda aka yi lokacin gwagwarmayar neman 'yancin kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata daga fararen fatar Afirka ta Kudun marasa rinjaye da ya zo karshe a shekara ta 1994, da zaben marigayi Nelson Mandela a matsayin shugaban kasar.

Masu shirya gangamin adawa da shugaba Zuman sun ce, wannan somin tabi ne kawai a jerin zanga-zangogin da zasu gudanar, har sai sun ga kwalliya ta biya kudin sabulu, na maido da martabar da aka san Afirka ta Kudun da ita.

 

Sauti da bidiyo akan labarin