1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Kwango na yin tirjiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 27, 2017

'Yan adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun sanar da cewa mutane da dama sun sanya hannu kan takardar kin amince wa da kwaskwarimar da aka yi wa dokokin zaben kasar.

https://p.dw.com/p/2pzoU
Adawa da Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Kwango
Adawa da Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyyar Dimokaradiyyar KwangoHoto: Reuters/T. Mukoya

Jam'iyyar adawar dai ta ce an yi kwaskwarimar ne domin cimma burin jam'iyya mai mulki ta Shugaba Joseph Kabila. Kakakin jam'iyyar adawar Christophe Lutundula ya nunar da cewa kwaskwarimar ta hana wasu da za su iya taka rawar gani wajen tsaya wa takara da Shugaba Kabila tsayawa takara, a yayin zabukan da za a gudanar a ranar 23 ga watan Disambar shekara mai zuwa. A baya dai an amince da gudanar da zaben a karshen wannan shekara ta 2017 da muke ciki bayan cimma yarjejeniya da 'yan adawa,  kafin daga bisani a dage shi zuwa karshen shekara mai zuwa.