1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa na ci gaba da zanga-zanga a Guinea

Binta Aliyu Zurmi MAB
October 15, 2019

Gamayyar kungiyoyin adawan Guinea sun yi kira da a ci gaba da gudanar da zanga-zanga don tilasta wa shugaban kasar Alpha Conde janye yunkurinsa na yi ma kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska don ci gaba da mulki.

https://p.dw.com/p/3RL86
Guinea Conakry | Proteste & Ausschreitungen
Hoto: Getty Images/AFP/C. Binani

Gamayyar Kungiyoyi na FNDC na son dakatar da yunkurin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara wanda zai bai wa shugaba mai ci Alpha Conde damar tsayawa takara. Shugaban mai shekaru 81 na son neman wa'adi na uku a zabe mai zuwa a shekarar 2020.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan mutuwar wasu fararen hula biyar a arangamar tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda. Sai dai a cewar jam'iyyar ta adawa mutum kusan dari ne suka rasa rayukansu a rigingimu tun bayan da shugaban ya dare mulki a shekarar 2010.

A Jumma'ar da ta gabata 'yan majalisa da ke bangaren adawa 53 sun janye daga majalisa a wani yunkuri na kin amincewa da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.