1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Zimbabwe na nuna rashin gamsuwa

August 22, 2014

Madugun adawa a Zimbabwe Morgan Tsvangirai, ya yi gargadin cewa mai yiwuwa jam'iyyarsa ta shirya zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Robert Mugabe

https://p.dw.com/p/1CzWj
Richard Tsvangirai Ministerpräsident Simbabwe
Hoto: Getty Images

Tsvangirai ya ce tun zabukan bara gwamnatin Mugabe ta gaza cika alkawarinta na shawo kan rikicin tattalin arzikin da ya addabi kasar, musamman rashin aikinyi da samar da ababen more rauywa ga talakawa.

Wannan furuci na Tsvagirai na zuwa ne bayan da 'yan sanda suka kama wasu masu fafutuka daga jam'iyyarsa ta MDC suka yi musu duka, sakamakon shiga titunan da suka yi ranar litini, suna zanga-zanga suna kuma kira ga shugaba Mugabe da ya cika alkawarin da yayi bayan zabe, na samar da guraben aiki milliyan biyu a duk fadin kasar.

A makon da ya gabata, lokacin wani taro da ta yi, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi godo da kungiyar kula da cigaba da raya tattalin arzikin kasashen Kudancin Afirka, wato SADC, da su dauki kwararan matakai kan wadanda ke take 'yancin walwalar jama'a a kungiyar ta su

A kasar Zimbabwe dai, 'yan sanda ne ke bayar da izinin gudanar da zanga-zanga kuma sukan ladabtar da duk wanda ya ki mutunta umurninsu.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe