'Yan adawa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ƙaurace wa shiga sabuwar gwamnati.
April 2, 2013Gwamnatin ta haɗin kan ƙasa wace pirayim mistan Nicolas Tiangaye ya naɗa, ta ƙunshi manbobi 34 waɗanda suka haɗa da wakilan tsohuwar ƙungiyar 'yan adawar da na yan' tawaye da kuma na ƙungiyoyin fara hula.
Yan adawar sun ce suna buƙatar samun ƙarin haske akan gwamnatin riƙon ƙwarya
A cikin wata sanarwa da suka bayyana haɗin gwiwar jam'iyyun siyasar da suka yi adawa da tshohuwar gwamnatin Francois Bozize, wanda yan tawayen Seleka suka hamɓarrar a cikin watan jiya. Wadanda suka haɗa da MLPC sun sanar da cewar sun dakatar da shiga gwamnatin. Josephe Benduga Tsohon magajin garin Birnin Bangui, na ɗaya daga cikin shika shikan ƙawancen jam'iyyun siyasar. Ya ce : ''Ni kai na, da na ke yin magana da ku minista ne, na kiwo. Ya ce kuma ban halarci wannan zaman taro na majalisar ministocin ba, tare da ni a kwai ministocin da ba su halara ba. Amma ya ce duk da haka a kwai wasu daga cikin mu, waɗanda suka shiga taron, ya ce wannan ya yi ruwan su, ya ce kuma jam'iyyun siyasar da waɗannan maya gurbi suka fito alhaki ya rattaya akan su na ɗaukar nauyin lamarin.''
Taron ƙasashen yankin Tsakiyar Nahiyar Afirka zai tattauna rikicin siyasar ƙasar
Shida daga cikin ministocin guda tara na yan adawa a ciki haɗa pirayim ministan sun jadada kasancewa a cikin gwamnatin haɗin kan ƙasar. Tare da bayyana aniyarsu ta yin aiki domin ci gaban ƙasar da ke fama da matsalar talauci. Duk kuwa da arzikin ma'adinai da Allah ya albarkaci ƙasar da su, Josephe ya bayyana dalilansu na ƙauracewa gwamnati. Ya ce: ''Buƙatar mu ga Tchangaye shi ne cewar ya kamata a fayace mana dala dala tsarin da aka yi na gwamnatin riƙon ƙwaryar domin kada a bar mu cikin duhu, ta yada dukkanin sauran sassan da suka halarci yarjejeniyar Libreville zasu amince da tsarin.''
Yanzu haka dai al'amura sun fara daidaita a ƙasar inda bankuna da shaguna suka sake buɗewa a daidai lokacin da ƙasashen yankin na Tsakiyar Afirka zasu soma wani taro a gobe a birnin Ndjamena wanda zai tattauna rikicin siyasar na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto , sannan kuma a kwai rahoton da Lateefa Mustapha Ja'afar ta haɗa mana akan Jana'izar Sojojin Kasar Afrika ta Kudu 13 da aka kashe a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman