′Yan adawa a Guinea sun kaurace wa majalisar dokoki | Labarai | DW | 18.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa a Guinea sun kaurace wa majalisar dokoki

'Yan adawar na zargin Shugaba Alpha Conde da amfani annobar Ebola a matsayin hujjar dage lokacin gudanar da zabe.

Guinea Wahl 2013

Shugaba Alpha Conde na Guinea

Jam'iyyar adawa a kasar Guinea ta janye wakilanta daga majalisar dokoki da ke birnin Konakry, sannan ta ce ba ta amince da hukumar zaben kasar ba don nuna adawa da lokacin zaben shugaban kasa. Madugun 'yan adawa Cellou Dalein Diallo ya ce sun dauki matakin janye wakilansu 49 daga majalisar dokokin har sai abin da hali ya yi. 'Yan adawar na zargin Shugaba Alpha Conde da amfani annobar Ebola da ta barke a kasar a matsayin hujjar dage lokacin gudanar da zaben. Suna kuma zarginsa da kin shiga tattaunawar neman mafita daga wannan dambarwa. A makon da ya gabata hukumar zaben kasar ta ce a ranar 11 ga watan Oktoba za a gudanar da zaben, biyo bayan shakku da aka nuna game da lokacin shirya zaben.