′Yan adawa a Guinea sun amince da shirin zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa a Guinea sun amince da shirin zaben shugaban kasa

Karkashin matsayar za a yi zaben shugaban kasa a watan Oktoba mai zuwa, inda yanzu shugaban zai nada Magadan gari da shugabannin kananan hukumomi

'Yan adawa na kasar Guinea Conakry sun tabbatar da cewa sun amince da matsaya tare da Shugaba Alpha Conde, wanda zai nada sabbin magadan gari da shugabannin kananan hukumomi, cikin shirin tattaunawar da ta share hanyar zaben a watan Oktoba mai zuwa. tsohon Firaminista Sidya Toure wanda yake bangaren 'yan adawa ya tabbatar da haka bayan ganawa da shugaban.

Tun farko 'yan adawa sun zargi gwamnati da saba yarjejeniyar gudanar da zaben kananan hukumomi kafin zaben shugaban kasa, saboda za su iya taimaka wa Shugaba Conde lokacin zaben kasa baki daya. Karkashin tsarin za a gudanar da zaben shugaban kasar ranar 11 ga watan Oktoba mai zuwa. Shugaba Alpha Conde ya lashe zaben shekara ta 2010 wanda ya mayar da kasar ta Guinea Conakry da ke yankin yammacin Afirka bisa tafarkin demokaradiyya, bayan shafe shekara da shekaru karkashin kama-karya da mulkin sai Madi ka ture.