Yamutsin siyasa a Yamen | Labarai | DW | 19.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yamutsin siyasa a Yamen

Fada ta kaure a fadar shugaban kasar da ke Sana'a, inda sojojin da ke gadin shugaban kasa ke fafatawa da 'yan tawayen Huthi, lamarin da gwanati ta ce yunkurin juyin mulki ne

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa ana can ana gumurzu tsakanin sojin kasar da mayakan Huthi. kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran Faransa wato AFP ya labarta, a halin da ake ciki mayakan na Huthi da ake alakantawa da mabiya darikar Shi'a ne, na ikirarin karbe iko da sansanin soji dake kula da fadar shugaban kasan.

Ministar yada labaran kasar ta Yamen Nadiya Al-saqaf, ta danganta wannan harin da yunkuri na kifar da gwamnatin kasar. An dai tabbatar da mutuwar mutum guda, sai dai ba a bayyana bangaren da ake zargi da yunkurin na kifar da gwamnati ba. Tun watan Satumba ne dai 'yan tawayen Huthi suka kame wani bangaren Sana'a babban birnin kasar ta Yamen.

Mawallafi: Muntaqa Ahiwa

Edita: Usman Shehu Usman