1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Ruwanda: Batu a jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal YB
April 5, 2019

An yi kiyasin cewa mutane dubu 500 zuwa miliyan daya ne aka kashe a tsukin watanni uku na kisan kare dangi a Ruwanda daga ranar shida ga watan Afrilun 1994. Shekaru 25 kenan kawo yanzu.

https://p.dw.com/p/3GN5Z
Ruanda Gedenkstätte an Völkermord in Nyamata
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Ruwanda inda a karshen wannan mako ake cika shekaru 25 da aukuwar kisan kare dangi a kasar.

A labarin da ta buga mai taken bin sahun kisan kare dangi jaridar ta Die Tageszeitung ta shekaru 25 bayan kisan kare dangi a Ruwanda har yanzu akwai gawarwaki 800 da aka shafa musu sinadari na musamman da ke hana gawa rubewa a wani aji na tsohuwar makarantar sakandaren fasaha ta Murambi da ke kudu maso yammacin kasar ta Ruwanda. Jaridar ta ce gawarwakin da ba a san ko su wane ne ba, suna zaman shaida ta ta'asar da ta auku daga ranar shida ga watan Afrilun shekarar 1994. Sai dai yanzu bisa ga taimakon Jamus an fara aikin tantance asalin gawarwakin da yawancinsu na yara ne kanana. An yi kiyasin cewa mutane dubu 500 zuwa miliyan daya ne aka kashe a tsukin watanni uku na kisan kare dangi a Ruwanda daga ranar shida ga watan Afrilun 1994, inda 'yan kabilar Hutu masu rinjaye suka hallaka kimanin kashi uku cikin hudun na 'yan kabilar Tutsi marasa rinjaye da kuma wasu 'yan Hutu masu sassaucin ra'ayi.

Jacques Nkinzingabo
Jacques Nkinzingabocikin wadanda suka tsira a yakin RuwandaHoto: Privat

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta sake lekawa kasar Mozambik ne tana mai cewa makonni uku bayan bala'in guguwa da ruwa sama har yanzu mutane a Mozambik na cikin mawuyacin hali, inda masu aikin taimako ke gargadi game da tasirin iftila'in na dogon lokaci da ka iya yin sanadin rayukan dubbai na mutane. Jaridar masu aikin ceto na amfani da karnuka masu sunsuna da aka shiga da su Mozambik din daga Afirka ta Kudun a aikin gano gawarwaki. Ko da yake an fara aikin sake gina wasu wuraren kamar a birnin Beira da guguwar ta fi yin ta'adi, amma har yanzu babu hasken wutar lantarki da ruwan sha. Da yawa daga cikin mazauna birnin ba su san inda 'yan uwansu suke ba.