Yakin neman zaben shugaban kasa a Tunisiya | Labarai | DW | 01.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yakin neman zaben shugaban kasa a Tunisiya

A wannan Asabar din ce (01.11.2014) aka soma yakin neman zaben shugaban kasar Tunisiya, wanda shi ne na farko tun bayan juyin juya halin da ya wakana a wannan kasa.

A kalla dai 'yan takara 27 ne zasu fafata a ranar 23 ga watan nan na Novemba, inda daga cikin su a kwai Shugaban mai barin gado Moncef Marzouki, da mace guda mai suna Kalthoum Kannou, wadda take alkalin shari'a ce, da kuma tsofin Ministoci na zamanin mulkin tsofon Shugaban kasar Zine El-Abidine Ben Ali, sai kuma tsofon Firamistan kasar Béji Caïd Essebsi, dan shekara 87 da haihuwa wanda ake ganin zai iya lashe zaben, ganin yadda Jam'iyar sa ta Nidaa Tounes ta samu babban rinjaye a zaben 'yan majalisun dokokin kasar. Idan dai ba wanda ya samu kuri'un da suka dace a zagaye na farko, to za'a je zagaye na biyu a karshen watan Disamba mai zuwa. Tun lokacin da wannan kasa ta samu mulkin kai a shekarar 1956 shugabannin kasa biyu ne kawai sukayi mulki, da suka da Habib Bourgiba da aka kifar da gwamnatin sa a 1987 da kuma Ben Ali wanda ya kifar da gwamnatin ta Bourgiba, da shi kuma al'umma ta kifar da tashi gwamnatin.