Yakin neman zabe a kasar Venezuela | Labarai | DW | 02.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yakin neman zabe a kasar Venezuela

Dan takarar jam'iyar da ke mulki Nicolas Maduros ya kaddamar da yakin neman zabensa a mahaifar Chavez, yayin da madugun adawa Henrique capriles ya yi a gabashin Venezuela.

Shugaban kasar Venezuela mai rikon kwarya Nicolas Maduro ya kaddamar da yakin neman zabensa a sabaneta da ke zama mahaifar tsohon shugaba marigayi Huguo Chavez. Ranar 14 ga watan afrilun 2013 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa, sama da wata guda bayan mutuwar Chavez sakamakon cutar kansa da ya yi fama da ita. Shi dai dan takaran jam'iyar da ke mulki ya tahallaka yakin neman zabensa akan manufofin gurguzu da wanda ya gabace shi ya sa gaba.

Shi ma dai madugun 'yan adawan Venezuela Henrique Capriles ya kaddamar da yakin neman zabensa ne a Monagas da ke gabashin kasar. Duk wasu kididdigar jin ra'ayin jam'a da aka gudanar sun nunar da cewa Nicolas Maduro ne zai lashe zaben na shugaban kasa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman