Yakin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
January 13, 2014Talla
Kakakin majalisar rikon kwaryar kasar Alexandre-Ferdinand Nguendet ne ya sanar da hakan, inda ya sha alwashin kawo karshen tashin hankalin da ya afku a kasar na tsahon makwanni da ya haddasa asarar rayuka da dama tare kuma da tilastawa dubban 'yan kasar dama 'yan kasashen ketare tsereawa domin tsira da rayukansu.
Kafa gwamnatin ta rikon kwarya dai ya biyo bayan sauka daga kan karagar mulki da shugaban kasar Michel Djotodia ya yi a makon da ya gabata, a wani yunkuri na kawo karshen zubar da jinin da ake fama da shi a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya tun bayan da ya jagoranci 'yan kungiyarsa ta 'yan tawayen Seleka suka kifar da gwamnatin Francois Bozize.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal