Yaki da masu tada tarzoma a Masar | Labarai | DW | 09.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaki da masu tada tarzoma a Masar

A yayin da Masar ke kai hari don kawar da masu tada tarzoma a Sina'i , wata kungiya a yankin ta dauki alhakin neman kissan wani jami'i a kasar.

Wata kungiyar mayakan sa kai dake arewacin zirin Sina'i na Masar, ta yi ikirarin cewar, ita ce ta kai hari, amma wanda bai yi nasara ba, da nufin kissan ministan kula da harkokin cikin gidan Masar. Dama dai wani bam da mayakan sa kai suka so tayarwa da nufin kissan Mohammed Ibrahim, ya janyo mutuwar wasu fararen hula dake kusa da wurin da suka tada bam din, game da haddasa rauni ga fiye da mutane 20.

A halin da ake ciki kuma, wasu jiragen yaki - masu saukar ungulu sun yi ta ruwan bama-bamai a wuraren da jami'an tsaron na Masar suka ce maboyar masu tada tarzoma ne a zirin na Sina'i - yini na biyu kenan - a jere a wannan Lahadin (08.09.13). Jami'an tsaron sun kara da cewar, manufar kaddamar da hare haren, ita ce fatattakar kungiyoyin sa kai, wadanda ke da alaka da kungiyar alQa'ida daga kauyuka daban daban da ke kan iyakar, inda suka ce mayakan suna da runbunan makamai, kuma suke neman samun gindin zama.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe