Yaki da kyamar masu Sida a kasar Lesotho | Himma dai Matasa | DW | 15.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Yaki da kyamar masu Sida a kasar Lesotho

Kasar Lesotho kasa ce da ta dade ta na gangamin yaki da yaduwar cutar HIV / AID ko Sida ga al'umma ta yadda za a daina kyamar masu cutar.

Moleboheng Rampou Youth 4 Peace

Moleboheng Rampou

A kowace Juma'a dai matasan da suka kafa kungiyar ta "Youth for peace" Moleboheng Rampou da Ma-lord Mefane sun kasance su na gudanar da shiri a radio a garin Maseru da ke kasar ta Lesotho dan fadakar da al'umma game da kaurace wa kyamar masu fama da larurar kuma a lokacin gabatar da shirin sukan ba al'umma dama su tofa albarkacin bakin su game da cutar ta HIV ko Sida. Wadan nan 'yan fafutuka dai suna bai wa radio mahimmanci wajen gabatar da gangamin wayar da kan al'umma kamar yadda daya daga ciki Moleboheng Rampou ta bayyana.

Lesotho Patienten in Klinik

Sashen kula da masu cutar Sida a Lesotho

"Radio wani Dandali ne mai kyau a irin wannan aiki da muke yi saboda nuna kyama ga al'umma da ke dauke da ciwon na HIV shi ke hanasu su fito suyi magana amma radio kan taimaka wa a ba su dama su yi magana ba tare da an gane su ba."

Al'ummar kasar Lesotho dai masu dauke da larurar Sida kan yi dar-dar wajen bayyana matsayin su saboda gudun abun da ka iya biyo baya na nuna kyama da wariya a gare su. Amma dalilin wannan kungiya ta yan fafutakar ganin sun wayar da kan al'umma, ana samun cigaba sosai, inda suka sha alwashin ganin sun ci-gaba da fadakar da jama'a, kuma sukan shiga har makarantu dan fadakar da Dalibai matasa kamar yadda daya daga cikin yar fafutukar Ma-lord Mefane ta bayyana a lokacin da suke wani gan gami a jami´ar kasar ta Lesotho.

Mamahou, Lesotho Patienten in Klinik

Sashen kula da masu cutar Sida a Lesotho

"Tace Youth for peace dandali ne da matasa ka iya hadu wa wuri guda dan tinkarar kalubalen da ke gaban su. Daga cikin su kuwa shi ne cutar HIV. kuma kunsan cewa yanzu mune na biyu?"

Tlecase Makhele, wani mai dauke da cutar HIV ne ya bayyana irin yadda yake muamala da al'umma.

"Ina jin takaici yadda Mutane ke nuna kyama a gare ni saboda suna ganin ina dauke da kwayar cutar hakan kansani nayi cikin kunci kuma sun maidani saniyar ware basayin komai da ni."

Wannan gangami da wadan nan matasa ke yi bai tsaya a birnin kasar ta Lesotho kadai ba sun fadada shi har zuwa yankunan karkara domin yanzu haka akalla matasa kusan 200 ke cikin masu yin wannan aiki.