Yaki da cin hanci a jamhuriyyar Benin | Labarai | DW | 22.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaki da cin hanci a jamhuriyyar Benin

A kokarin dakile matsalar yiwa tattalin arziki zagon kasa, gwamnatin jamhuriyyar Benin ta tsare ministan muhalli.

Der Präsident von Benin, Thomas Boni Yayi, spricht am Sonntag (04.11.2007) im Kloster Eberbach bei Eltville bei einer Pressekonferenz. Bundespräsident Köhler hatte zur dritten von ihm veranstaltete Afrika-Konferenz unter dem Titel Herausforderungen des Wandels - afrikanische und deutsche Antworten geladen. Foto: Frank Rumpenhorst dpa/lhe +++(c) dpa - Report+++

Thomas Boni Yayi

A wannan Talatar ce hukumomin jamhuriyyar Bene da ke yankin yammacin Afirka suka cafke ministan kula da harkokin muhalli da raya yankunan karkara a kasar bisa zargin yin almubazzaranci da kudaden da suka danganci shirin gina sabuwar majalsar dokokin kasar.

Blaise Ahanhanzo-Glele, ya zama mutum na tara cikin jerin mutanen da hukumomin na kasar Benin suka tsare a cikin wannan watan akan aikin gina sabuwa majalisar dokokin, wadda gwamnati ta kashe fiye da kudi miliyan dubu 12 na CFA, wato kwatankwacin Euro miliyan 18, ko kuma dalar Amirka miliyan 24.

A da dai ministan wani jigo ne a jam'iyyar adawar kasar, gabannin sauya sheka tare da shiga cikin gwamnatin shugaba Thomas Boni Yayi, bayan sake zaban shugaban a shekara ta 2011 domin jagorantar kasar Benin - mai yawan al'umma miliyan tara.

Sai dai kuma akwai wadanda ke zagin cewar shugaba Yayi na kokarin dakile wadanda ya ke ganin abokan gabarsa na siyasa ne, amma shugaban, ya sha na'na'ta cewar yana daukar matakan shawo kan matsalar cin hanci da rashawa ne.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou