Yajin aikin malamai a Afirka Ta Kudu | Labarai | DW | 24.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin malamai a Afirka Ta Kudu

Kungiyar malamai a Afirka Ta Kudu ta shiga yajin aikin neman ministar Ilimin kasar tayi murabus.

South African Democratic Teacher's Union member clash with police during their protest in Johannesburg, South Africa on Thursday Aug. 19, 2010. Police fired rubber bullets on protesting teachers throwing bricks and stones and nurses tore down a gate at a hospital as a nationwide civil servants' strike for higher wages took hold in South Africa on Thursday.On the second day of the strike for higher wages, teachers in the red T-shirts of their union scattered as police fired to stop them from blocking a stretch of highway during a protest in Johannesburg.(AP Photo/Themba Hadebe)

A wannan Larabar ce (24.04.2013) kungiyar malaman makaranta a kasar Afirka Ta Kudu ke yin yajin aikin gama-gari na yini daya game da gudanar da jerin gwano domin neman ministar kula da harkokin Ilimi a kasar ta yi murabus. Kungiyar, wadda ke zama reshe a cikin hadaddiyar kungiyar ma'aikata ta kasar, ta ce kimanin malamai 25,000 ne ke shiga a dama da su cikin jerin gwanon, da kuma yajin aikin.

Dama kuma kungiyar ma'aikata a kasar, ta nemi ministar Ilimin farko, Angie Motshekga tare da darekta janar a ma'aikatar kula da sha'anin Ilimin, Bobby Soobrayan su yi murabus, bisa tabarbarewar sha'anin Ilimi a kasar.

Sai dai kuma ma'aikatar kula da sha'anin Ilimi a kasar ta Afirka Ta Kudu ta yi barazanar ladabtar da duk wani malamin makaranta ko kuma shugaban makarantar Sakandaren daya kuskura ya shiga cikin yajin aikin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman