Yajin aikin gama gari ya gurgunta harkoki a yankin Kataloniya | Labarai | DW | 03.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gama gari ya gurgunta harkoki a yankin Kataloniya

Komai ya tsaye cak a yankin Kataloniya sakamakon yajin aiki na gama gari da aka kira don adawa da matakan karfi kan masu zabe.

Al'ummar yankin cin gashin kai na Kataloniya da ke a kasar Spaniya sun tsunduma wani yajin aiki na gama gari don nuna fushinsu da matakan karfi da 'yan sanda suka dauka kansu a lokacin kuri'ar raba gardama ta ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce an rufe kusan dukkan makarantu da kantuna da wuraren cin abinci a Barcelona babban birnin yankin. Kuma mutane dubu biyu sun yi zanga-zanga a gaban ginin jam'iyyar PP ta 'yan ra'ayin mazan jiya da ke jan ragamar mulki a Spaniya, suna masu zargin jam'iyyar da laifin mummunar arangamar da aka yi lokacin kada kuri'ar, inda mutane 900 suka jikkata.

A yankin gaba daya mutane kimanin dubu 300 ne suka shiga zanga-zangar ta wannan Talata.

Gwamnatin yankin ta ce kimanin kashi 90 cikin 100 na al'ummar yankin suka kada kuri'ar amincewa da samun 'yancin kai daga Spaniya. Kimanin kashi 42 cikin 100 na 'yankin mai yawan mutane miliyan 5.3 da suka cancanci kada kuri'a, suka yi zaben, wanda gwamnatin Spaniya ta ce haramtacce ne.