Yajin aikin gama gari a kasar Kwango | Labarai | DW | 16.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gama gari a kasar Kwango

'Yan adawa a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango sun kira wani yajin aikin gama gari a wannan Talata wanda hakan ya gurgunta harkoki a Kinshasa babban birnin kasar.

Makarantu da ma jami'o'i sun kasance a rufe sannan kuma zirga-zirgar ababen hawa da a da aka saba fuskantar cunkoso a birnin na Kinshasa, ta kasance babu wannan cinkoson abun da ke nunin cewa yajin aikin ya karbu. Sai dai kuma yajin aiki bai samu cikakar karbuwa ba a Lubumbashi birni na biyu a kasar ta Kwango.

Bayan da aka shafe tsawon awowi babu ababan hawa, wajejan karfe 10 agogon kasar an fara samun motocin safa-safa da ke daukan mutane cikin birnin. Sai dai akasarinsu suna yawon ne ba tare da mutane a cikin su ba a acewar wata majiya ta kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP.

Sai dai hukumomin sun ce za su dauki mataki a kan ma'aikatan da suka yi wannan yajin aiki.