Yajin aikin gama gari a Ethiopiya | Labarai | DW | 05.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gama gari a Ethiopiya

A birnin Addis Ababa na Ethiopiya shaguna da kantuna da makaratun sun kasance a rufe a sakamakon yajin aikin gama gari da kungiyoyin masu fafutuka da na 'yan siyasa suka kira domin nuna damuwa da dokar ta baci.

Daga cikin yankunan da yajin aikin ya fi samu karbuwa har da yankin 'yan kabilar Oromo kabila mafi rinjaye a kasar, kana masu adawa da gwamnatin. An dai kafa dokar ta bacin ne a cikin watan da ya gabata  a jajibirin da firaminista Hailemariam Desalegn ya yi marabus. 

Zanga-zangar nuna kyamar gwamnati, da 'yan kabilar na Oromo suka soma yi tun a shekara ta 2015 zuwa 2016 ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 940.