1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yahudawa uku sun hallaka cikin harin rokoki

November 15, 2012

Ana ci gaba da samun tashin hankali tsakanin Palesdinawa da Yahudawa, wanda ke barazana ga zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/16jre
Hoto: Reuters

Yahudawa uku sun hallaka cikin harin rokokin da tsagerun Palesdinawa su ka cilla daga yankin Zirin Gaza na Palesdinawa, a wannan Alhamis.

Wannan ya zo lokacin da hare hare Isira'ila ta sama su ka hallaka Palesdinawa 13, kuma Isira'ila ta ci gaba da kai hare haren kan wuraren da ta ke zargin tsagerun Palesdinawa da amfani da su wajen kaddamar da hare hare.

Tuni Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kirar neman ganin kawo karshen rikicin.

A cikin wani jawabi shugaban kasar Masar Mohammad Mursi, ya ce hare haren Isira'ila kan Zirin Gaza ba abu da za a amince da shi ba.

Mawallaf: Suleiman Babayo
Edita: Usman shehu Usman