1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Abu Namu: Kalubalen yara mata a lokacin al'ada

December 7, 2020

Rashin samun auduga don amfani a lokacin jinin al'ada ya janyo koma baya matuka ga ilimin yara mata, musamman ga wadanda ke rayuwa a yankunan karkara a kasashen duniya masu tasowa.

https://p.dw.com/p/3mLxf

Yara mata da suka balaga mussaman a yankunan karkara na fuskantar matsalar rashin samun damar amfani da audugar mata yayin al'adarsu ta wata-wata. Bincike dai na nuna cewa ‘yan mata musamman ‘yan shekaru 15 zuwa 19 ba su iya zuwa makaranta a duk lokacin da suke jinin al’ada a dalilin rashin kudin siyan audugan da za su saka.  An yi kiyasin cewa tsadar audugar ta janyo mata fiye da miliyan daya suna fashin makaranta har na tsawon makonni shida a duk shekara.


Duk da irin tarin kungiyoyi da ke tallafawa mata sai dai ba kasafai ake samun da dama da ke yunkuri na rabawa mata auduga ba, ko da yake ba kasafai ake samun mata na fitowa fili su na magana a kan abin da ya shafi al'adar su ta jinin haila ba. Ga Zainab Naseer Ahmed da ke jagorantar Girl child Initiative and commuinty engagement hakan bai hana ta yin wani yunkuri na taimaka wa mata mussaman na karkara da makarantu ta wannan bangaren ba. Wannan matsala da ke ciwa kasashe da dama tuwo a kwarya dai da alama ta zama labari a kasar Scotland, don a baya-bayan kasar ta zamo kasa ta farko a duniya da ta samar da audugar al'ada ta mata kyauta ga kowa bayan shan fafutukan amincewa da kudurin dokar da aka gabatar a gaban majalisar kasar tun a shekarar 2016.