Yadda dabbobi ke yi wa kansu magani
Manazarta sun lura da yadda gwaggon birin Orangutan ke yi wa kansa maganin cuta a fuska. Dabbobi suna da hanyoyi da dama na taimakon junansu. Mutane sun kwaikwayi wasu daga cikin dabarun.
Ganyen bishiya domin waraka
Manazarta sun lura da yadda gwaggon birin Orangutan a Indonesiya ya warkar da kansa ta amfani da ganyen bishiya. Birin ya tauna ganyen ya matsa ruwan a kan ciwon sannan ya manna ganyen akan ciwon a matsayin flasta, cikin mako guda ciwon ya warke. Ganyen bishiyar da ake kira Akar Kuning, mutane na amfani da shi a Indonesiya a matsayin magani.
Amara ta maganin dabbobi
Dabbobi na amfani da magunguna da ake da su a dazuka wajen warkar da cututtuka ko kashe kwari. Masu bincike sun gano yadda gwaggon biri a Gabon da ke yammacin Afirka suke warkar da cututtukansu, ba da ganyayyaki ba kawai.
Amfani da kwari wajen magani
Gwaggon birai da dama a gandun dajin Loango, manazarta sun lura da yadda suke kamo kwari da ke yawo a sama su sa tsakanin labbansu su tauna sannan su sa kwaron a cikin ciwon da suka ji. Abin la'akari shi ne ba kawai suna warkar da ciwon su ba ne kadai, suna ma warkar da 'yan uwansu kamar yadda ake gani a nan. Wannan ya nuna birrai suna iya gudanar da al'adar zamantakewa da za ta amfanar da wasu.
Daukar darasi daga dabbar bear
Bakar dabbar bear ta Amirka ta san tasirin saiwar osha wajen magani. Masanin tsirrai da hallitu Shawn Sigstedt, wanda ya yi nazarin rayuwar dabbobi a arewacin New Mexico, ya gano suna amfani da saiwa wajen warkar da cuttukansu na gabbai. Ya ce mutanen yankin sun fara gano tasirin warakar daga dabbobin na bear bayan da suka lura da yadda suke amfani da shukar daruruwan shekaru da suka wuce.
Yadda karnuka suke amfani da maganin sakin ciki
Watakila idan ka na da karenka akwai yadda yake yi wa kansa magani. Karnuka su na cin ciyawa idan cikinsu yana ciwo. Yawanci su kan amayar da ciyawar bayan dan wani lokaci ba tare da ta narke ba. A wajensu ta haka suke fitar da tsutsotsi da kwayoyin cututtuka.
Wani tsunstu yana wanka da sinadarin formic acid da kananan kwari ke fitarwa
Masu nazarin bincike na da masaniya kan tsuntsaye fiye da 200 da ke zama a kan reshen bishiya karkashin shekar kwari ko gidan tururuwa suna motsa fikafikansu don jawo hankalin kwarin. Ta haka tsuntsayen suke lullube kansu da sinadarin formic acid da kwarin ke fitarwa inda ta haka suke kawar da kwayoyin cuta daga jikindu da fikafikansu.
Yadda Giwaye ke taimakon haihuwa
Giwa na daukar ciki tsawon watanni 22 fiye da dukkan wata dabba. Shi ya sa suke shirya fitar jariri idan lokacin ya yi. A Kenya a kan ga Giwaye masu tsohon ciki suna ratse hanya don cin rassan wasu itatuwa, jim kadan sai su haihu. Matan Kenya su ma suna amfani da itaciyar don taimakawa mai nakuda wajen haihuwa.
Amfani da mushroom don maye
Bayan warakar kai da kai, dabbobi suna kuma amfani da tsirai don buguwa ko maye. Shanun dawa a Finland da Siberia su kan bugu idan suka ci wani haki mai suna Amanita muscaria, wanda kuma ake kira amanita. Mutanen Sami suna amfani da hakin laimar kwadi (mushroom) wajen kiwata shannun dawa don taimaka musu wajen yin magana da dabbobin.
Yanayin suma na puffer fish
Yayin da ya ke daukar hoto na wani shirin BBC masu bincike sun lura Dolpin suna wasa da kifaye puffer suna motsawa su yi gaba su yi baya a tsakaninsu har kusan rabin sa'a. Su kan bar kifin na puffer ya tsira sabanin sauran da suka kamawa su cinye. Kifin na Puffer da ke cikin halin gigita kan fitar da wani sinadari wanda nan da nan yake sumar da dolpin ya sanya shi ya nutse a karkashin ruwa.