Yaa Nana Asantewaa -Jarumar sarauniya | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 17.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Yaa Nana Asantewaa -Jarumar sarauniya

Yaa Nana Asantewaa ta yi fice a kan rawar da ta taka a fage na jarumta a yakin kujerar gwal wato Golden Stool. Mace ce mai jajircewa. A baki dayan rayuwarta ta yi kokari wajen kare daularta.

DW Videostill Projekt African Roots | Yaa Asantewaa, Ghana (Comic Republic)

Yaa Asantewaa: Jarumar Sarauniya

Ta rayu tsakanin shekarar 1840 a Besease, daular Ashanti ta kasar Ghana a yanzu zuwa 17 ga watan Oktoba 1921 a Seychelles.

 

Abin da ya sa ta yi fice: 

Ta zaburar tare da ba da taimako ga abin da a yau ake kira da yakin kujerar gwal. Wannan kujerar yaki har yanzu na zama abin alfahari ga al'ummar Ashanti. Wakilin Birtaniya a wancan lokacin, Sir Frederick Mitchell Hodgson ya nemi a ba shi wannan kujera ya zauna a madadin sarauniyar Ingila.

Ta mayar da martani ga mazajen Ashanti dangane da bukatar wakilin Birtaniya tana mai cewa:

"[…]Da gaske ne jarumtakar al'ummar Ashanti ta gushe? "Na yi mamaki matuka, ba zai yi wu ba, na tilas in bayyana hakan! Idan ku mazan Ashanti ba za ku ja gaba ba, mu za mu iya, zan kira 'yan uwana mata mu yaki wadannan Turawa. Za mu yi yaki har sai dayanmu da ya yi saura ya fadi a fagen daga. Idan ku shugabanni ba za ku iya fada ba za mu sauya sutura ku karbi tawa na karbi taku."

- Kasancewarta wadda sarakunan Ashanti suka sanya ta jagoranci yaki, ta kasance mace ta farko kana guda daya tilo da ta kasance ja gaba a filin daga da bayar da shawarwari da sabunta kayan yaki ga sojojin Ashanti a yayin da take da shekaru 60 a duniya!

 

Abin da ta bari: 

Yaa Asantewa babbar abar koyi da alfahari ce a wajen yara mata da manyan mata a kasar Ghana da ma kasashen Afirka baki daya. Mata da dama da suka yi fice wajen nuna kwarewa a fagen da maza ke da rinjaye, a kan musu lakabi da Yaa Asantewaa a wani mataki na ba da karfin gwiwa da goyon baya.

A dubi bidiyo 01:59

Tarihin Yaa Nana Asantewaa

A shekarar 2000 an sadaukar da wani gidan tarihi don tunawa da wannan sarauniya a fagen yaki a garin Ejisu. Iyalanta sun taimaka kwarai wajen bayar da kayan da suka gada a wajenta da ma wadanda ta yi amfani da su lokacin da take raye da suka hadar da sutturu da kwanikan da aka ce a cikinsu take cin abinci. Sai dai abin takaici a watan Yuli na shekara ta 2004, gidan tarihin ya kama da wuta, inda gobarar ta lakume kayan cikinsa masu yawa, kana har yanzu ba a gyara shi ba.

An sanya sunanta ga makarantar sakandaren gwamnati ta farko a Kumasi, wato "Yaa Asantewaa Senior Girls' High School."

 

Pinado Abdu-Waba da Ramatu Mahmud Abubakar Jawando da Gwendolin Hilse ne su suka yi hidima wajen haduwar wannan labari. Shiri na musamman na bitar tarihin Afirka, wato "African Roots", shirin hadin gwiwa da cibiyar Gerda Henkel.

 

Sauti da bidiyo akan labarin