Yaƙi ya sake ɓarkewa a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango | Labarai | DW | 18.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙi ya sake ɓarkewa a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango

Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da hare haren da ƙungiyar 'yan tawayen M23 ta kai a yanki gabashin Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kwango

default

Kongo Flüchtlinge

A cikin wata sanarwa da wakilan kwamitin sulhun na Majalisar Ɗinkin Duniya suka baiyana,a wani taron gauggawa da suka kira sun buƙaci ƙungiyar ta 'yan tawayen M23 da ta daina kai hare haren.

Yan tawayen waɗanda suka yi dura mikiya a ƙauyen Kikumba, sun yi nasara ƙwace shi daga hannu sojojin gwamnatin;duk Kuwa da irin martanin da suka riƙa mayar wa da jiragen sama na yaƙi masu saukar ungulu.Duban jama'a na ta yin ƙaura daga garin domin kwararawa zuwa wasu ƙayuka na kusa saboda fargaban da suke da shi na ƙara dagulewar al'ammura

Tun da farko dai hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya ta Monusco da ke gudanar da aikin tabbatar da tsaro a yanki ta yi shelar wani hali na kasance wa cikin shirin ko ta kan kwana a yanki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman