Xi Jinping zai zama shugaba na din-din-din | Labarai | DW | 11.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Xi Jinping zai zama shugaba na din-din-din

Majalisar China ta bai wa Xi Jinping damar gudanar da salon mulkin sai Madi ka ture sakamakon kada kuri'ar soke tsarin wa'adi biyu na shugabanci da aka san kasar da shi.

Majalisar dokokin China ta kada kuri'ar amincewa da soke tsarin wa'adi na shugabancin kasar, abin da zai bai wa Xi Jinping damar yin tazarce da ma gudanar da salon mulkin sai Madi ka ture. 'Yan majalisa 2958 ne suka yi na'am da wannan tsari, yayin biyu suka nuna adawa sauran uku kuma sauka yi rowar kuri'unsu, makonni biyu bayan da jam'iyyar kasar mai ra'ayin gurguzu da ke muki ta gabatar da bukatar soke bin tsarin wa'adin, domin bai wa shugaba Xi Jinping damar ci gaba da shugabanci bayan karewar wa'adinsa a 2023.

Wannan tsarin zai sa a sanya muhimmanci jam'iyyar da ke mulki da kuma manufofin Xi Jinping a cikin kundin tsarin mulki. Sai dai ana ganin cewar zai bai wa gwamnatin China damar gallaza wa abokan adawarta, bisa zargin yin karar tsaye ga kundin tsarin mulki.Kasashen Turai sun danganta wannan tsari da koma baya ga China, yayin da shugaban Amirka Donald trump ya nuna goyon baya ga yunkurin na bai wa Xi Jinping damar zama shugaban China na din-din-din, lamarin da ya jawo masa kakkausar suka.