Wutar lantarki: Ministan makamashin Saliyo ya yi murabus
April 27, 2024Tun bayan dankwafar da shahadar aikin, ministan Alhadji Kanja Sesay, yaki cewa uffan dangane da murabus din da yayi tare da kin amincewa da bukatar tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.
Karin bayani: 'Yan sandan Saliyo sun zargi tsohon shugaban kasa Ernest Bai Koroma da kitsa juyin mulki
Tsohon ministan na makamashin kasar ta Saliyo na aiki ne karkashin kulawar shugaban kasar Julius Maada Bio tare da wasu mutanen biyu, acewar sanarwar murabus din ministan da hukumomin kasar suka bawa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Karin bayani: An bude wuta a gidan yarin Saliyo
Murabun din ministan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Saliyo ta rattaba hannu kan kwangilar Dalar Amurka milyan 18.5 da wasu kamfanonin kasar Turkiyya guda biyu domin samar da hasken wutar lantarki a fadin kasar.