1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Wuta kusa da ginin majalisar Amirka

Suleiman Babayo USU
January 18, 2021

Wuta ta tashi a wani gini da kusa da majalisar dokokin Amirka abin da ya janyo kwashe mutane a ginin majalisar na wani lokaci.

https://p.dw.com/p/3o5ut
USA | Vor Amtseinführung des designierten US-Präsidenten Biden
Hoto: Andrew Caballero-Reynolds/AFP

An rufe zauren majalisar dokokin Amirka na wani lokaci sakamakon hayaki da aka gani daga wani gini da ke nesa da wurin, lokacin da ake aikin kwaji kan rantsar da sabon Shugaba Joe Biden.

Hukumomin tsaron Amirka sun ce babu wata barazana ga rayuwar mutane kuma sun yi imani babu barazana lokacin da za a rantsar da Joe Biden a jibi Laraba.

Tuni Shugaba mai barin gado Donald Trump ya ce ba zai halarcin bikin rantsuwar ba, abin da aka dade ba a gani ba a tsarin Amirka, amma mataimakin shugaban kasa mai garin gado Mike Pence zai halarci bikin rantsuwar tare da sauran tsaffin shugabannin Amirka.