Wuta daji ta yi ta′adi a Ostareliya | Labarai | DW | 04.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wuta daji ta yi ta'adi a Ostareliya

Wuta na ci gaba da ci a daji duk da lalata gidaje tare da jikata mutane da dama da ta yi a kudancin kasar Ostareliya

'Yan kwana-kwana na ci gaba gwagwarmayar kashe wutar daji da ta tashi a yankin kudancin kasar Australiya. Jami'ai sun ce fiye da gidaje 30 suka kone. Lamarin ya jikata mutane 22. An rasa amfanin gona mai yawa, yayin da ake ci gaba da kwashe mutane.

Kimanin 'yan kwana-kwana 2000 suke aikin neman kashe wutar dajin tare da amfani da jiragen sama masu saukar ungulu. Jami'ai sun ce zai dauki kwanaki kafin shawo kan wutar dajin.