WHO za ta gudanar da taro a kan cutar Ebola | Labarai | DW | 06.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO za ta gudanar da taro a kan cutar Ebola

Nan gaba a yau wakilan ƙungiyar lafiya ta duniya za su gudanar da taro a Geniva, domin nazarin samar da hanyoyin magance cutar Ebola.

Ana sa ran a wannan taro hukumar za ta bayyana cutar ta Ebola a matsayin anoba da ke yin barazana ga ƙasashen duniya. Kakakin ƙungiyar Tarik Jasarevic ya ce taron zai yanke shawara.

''Babban daraktan hukumar na son ya samu ra'a'yin kwamitin gaggawa na ƙungiyar, don jin ko barazanar ta cutar ta Ebola lamari ne, da ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa na ƙasa da ƙasa a kan sha'anin kiwon lafiya.''

Kawo yanzu cutar ta Ebola ta kashe mutane kusan 900 a ƙasashen Saliyio da Liberia da kuma Guinea.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita :Umaru Aliyu