1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta jingine gwajin Hydroxychloroquine

Abdullahi Tanko Bala
May 26, 2020

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta dakatar da gwajin kwayar maganinnan na hydroxychloroquine a matakin wucin gadi, maganin malaria wanda shugaba Trump yace zai iya warkar da cutar corona.

https://p.dw.com/p/3clH6
Schweiz Genf WHO Treffen | Tedros Adhanom Ghebreyesus
Hoto: picture-alliance/Xinhua/WHO

Hukumar lafiyar ta ce ta na bukatar kwararrun jami'anta su sake yin nazari sosai akan dukkan wasu bayanai da suka danganci maganin kawo yau.

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaidawa taron manema labarai cewa sun yi hakan ne sakamakon wata mukala da aka wallafa a makon da ya gabata da ya nuna cewa mutanen da ke shan maganin na hydroxychloroquine na iya kamuwa da ciwon bugun zuciya ko ma hadarin mutuwa baki daya.

A makon da ya gabata shugaban Trump yace yana amfani da maganin na  hydroxychloroquine duk da cewa ba shi da cutar ta corona.

Hukumomin kula da ingancin magunguna da abinci na Tarayyar Turai da na Amirka a watan Afrilu sun gargadi jami'an lafiya kada su yi amfani da maganin akan masu cutar corona a wajen asibiti ko wajen cibiyar binciken kimiyya saboda yana iya kasancewa da hadari matuka.