WHO na rigakafin polio a kasashen Afirka | Labarai | DW | 24.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO na rigakafin polio a kasashen Afirka

Hukumar Lafiya ta Duniya zata yi wa miliyoyin yaran Afirka allurar rigakafin cutar shan Inna bayan da mutane uku suka kamu da cutar da Polio a tarayyar Najeriya a shekarar da ta gabata.

Kasashe 13 na Afirka na shirin gudanar da allurar rigakfin cutar shan Inna ko Polio na bai daya a ranar Asabar, bayan da aka tabbatar da cewar mutane uku sun kamu da ita a shekarar da ta gabata a arewacin tarayyar Najeriya. Cikin wata sanarwa da ta fitar Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za a yi wa yara miliyan 116 rigakafin shan Inna a kasashen da dama ciki har da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Benin.

WHO ta nunar da cewar mutane hudu ne suka kamu da cutar Polio a cikin wannan shekara ta 2017, biyu a Afghanistan, biyu kuma a Pakistan. Sai dai kuma ta ce zata rubanya rigakafi a kasashen Afirka saboda kaurin suna da nahiyar ta yi a fannin yawan wadanda suka kamu da Polio.

Tarayyar Najeriya ta taba kasancewa a sahun gaba na kasashen da aka fi fama da Polio a duniya. Sai dai WHO ta cireta daga wannan rukuni tun a shekara ta 2015 bayan da ta dauki matakan da suka dace.