WHO: Cutar corona na kara yaduwa a duniya
September 18, 2020Talla
Kungiyar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi kan yadda cutar ke yaduwa cikin hanzari.
A matakan da suke dauka Birtaniya ta takaita tarukan jama'a yayin da Faransa ke shirin gabatar da wasu matakan takunkumi a manyan biranen kasar.
Mutane fiye da 948,000 suka rasu a fadin duniya a sakamakon cutar ta Covid 19 tun bayan da ta barke a China a shekarar da ta gabata.
Daraktan shiyyar nahiyar Turai na kungiyar lafiya ta duniya Hans Kluge yace ya kamata hukumomi su farga wajen yaki da cutar bisa karuwar yaduwar cutar da aka gani a wannan watan