1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WhatsApp: Yaki da yada labaran karya

Gazali Abdou Tasawa
January 22, 2019

Kamfanin WhatsApp ya sanar da daukar matakin takaice adadin sakonnin da mutun zai iya aikawa a lokaci guda a wani mataki na yaki da yada labaran karya. 

https://p.dw.com/p/3BwFI
WhatsApp Logo
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Stein

Sashen kula da aikawa da sakon kar ta kwana na kamfanin WhatsApp da ke zama wani reshe na kamfanin Facebook ya sanar da daukar matakin takaita damar raba sakonnin kar ta kwana a tsakanin jama'a a wani mataki na yaki da yada labaran karya. 

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, ya ce daga yanzu duk mai amfani da manhajar ta shafinsa na da damar raba sakon da ya samu ne ga mutane biyar ko rukunin mutane biyar kawai a lokaci daya, sabanin yadda mutum ke iya aika sako har ga mutane 20 a lokaci guda. 

Dama dai a watan Yulin da ya gabata kamfanin na WhatsApp ya dauki irin wannan mataki ga masu amfani da shfinsa a kasar Indiya inda ake da mutum miliyan 200 masu amfani da shafin na WhatsApp. 

Kamfanin ya dauki matakin ne  bayan da gwamnatin Indiyar ta soke shi da kakkausar lafazi bayan da wasu alkalumman kididdiga sun nunar da cewa akalla mutane 25 ne mutanen gari suka halaka a cikin fushi a cikin shekara daya a kasar sakamakon wasu sakonnin karya da aka rika yadawa ta shafin sada zumunta na WhatsApp.