Wata kotu a Afganistan ta hukunta wasu ′yan sanda | NRS-Import | DW | 19.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Wata kotu a Afganistan ta hukunta wasu 'yan sanda

Kotun ta samu 'yan sanda da laifin yin sakaci na rashin ba da kariya ga wata matar da wani gungun jama'ar ya kashe.

Wata kotu a Afganistan ta yanke hukuncin ɗaurin shekara guda na zama gidan yari ga wasu 'yan sanda guda 11 saboda ta samesu da laifin gazawa wajen hanna kisan wata matar a kan ƙaharu da aka yi mata cewar ta ƙona litafin Alƙurani mai tsarki.

Manyan hafsoshin 'yan sanda guda 19 kotun take zargi da rashin taɓuka wani abu domin ceto matar daga hannu jama'ar da suka yi ma ta taron dangin.Matar mai suna Farkhunda 'yar shekaru 27 wani gungun jama'ar ya yi mata kisan taron dangi a cikin watan Maris da ya gabata kafin daga baya suka ƙona gawarta.