1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanatoci 15 sun fice daga APC

Abdullahi Tanko Bala
July 24, 2018

Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar APC ya yi kamari inda wasu 'yan majalisar dattijai na jam'iyyar suka fice suka koma jam'iyyar adawa ta PDP.

https://p.dw.com/p/321WX
Gouverneur Kwankwaso besucht Baustelle in Kano Nigeria
Hoto: DW/T. Mösch

A Najeriya 'yan majalisar dattijai fiye da 15 na Jam'iyyar APC mai mulki sun fice daga Jam'iyyar sun koma babbar jam'iyyar adawa PDP a wani mataki da ake gani na kalubalantar takarar shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Shugaban Majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya sanar da hakan ba tare da yin wani karin haske ba.

Daga cikin sanatocin da suka fice daga jam'iyyar dai sun hada da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan Jihar Kano.

Matakin na zuwa ne yan makonni bayan da wani tsagi na jam'iyyar ta APC ya sanar a wannan watan cewa ya dawo daga rakiyar gwamnatin.