Wasu matan da aka sace a Borno sun tsere | Labarai | DW | 07.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu matan da aka sace a Borno sun tsere

Rahotanni daga jihar Borno dake Arewa maso gabashin tarayyar Najeriya na nuni da cewa 63 daga cikin matan da aka sace a watan da ya gabata sun tsere.

Daya daga cikin 'yan kato da gora da ke taimakawa wajen yakar 'yan Boko Haram a jihar ta Borno Abbas Gava ya bayyana cewa wani abokin aikinsa ya shaida masa cewa 63 daga cikin matan sun koma gida tun ranar Jumma'ar da ta gabata. Gava ya shaida wa manema labarai cewa matan sun samu nasarar tserewa ne a yayin da masu tsaronsu suka fita kai farmakin da suka saba.

Shi ma wani babban jami'in tsaro a jihar ta Borno da ya bukaci a boye sunansa ya tabbatar da nasarar tserewa gida da matan suka samu. Ko da a ranar Jumma'ar da ta gabata ma dai sai da aka yi musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da jami'an tsaro a garin Damboa na jihar ta Borno inda rahotanni ke cewa akalla sama da 'yan ta'addan 50 ne suka sheka barzahu yayin wannan fafatawar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe