Lafiya
An samu ci-gaba a neman maganin AIDS
July 6, 2019Talla
Kwararrun likitocin guda uku Prasanta K.Dash, da Rafal Kaminski, da kuma Ramona Bella da ke aiki a jami'o'in Nebraska da Philadelphia sun yi nasarar warkar da kaso daya daga cikin uku na berayen da aka yi gwajin kansu ta hanyar amfani da wasu fasahohin kimiyya na zamani guda biyu.
Wannan dai shi ne karo na farko a tarihi tun bayan gano cutar ta Sida a shekara ta 1983 da wasu likitoci suka yi nasarar warkar da cutar kan wata halitta. Har ya zuwa wannan lokaci dai magungunnan da ake amfani da su wajen yaki da kwayoyin cutar na HIV, na taimakawa ga rage kaifin kwayoyin cutar kawai amma ba kawar da su ba kwata-kwata.