Wasu jami′ai na Koriya ta kudu sun yi zanga-zanga | Labarai | DW | 23.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu jami'ai na Koriya ta kudu sun yi zanga-zanga

Wasu jami'an gwamnatin kasar Koriya ta kudu sun gudanar da zanga-zanga a yau juma'a sakamakon ziyarar da wani Janar na kasar Koriya ta Arewa zai  kai Pyeongchang.

Masu zanga-zangar dai sun yi kira ga gwamnatin kasar ta Koriya ta Kudu da ta zartar masa da hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon zargin da ake masa da sanadiyyar nitsewar wani jirgin yakin Koriya ta Kudu a shekara ta 2010.

Janar  Kim Yong Chol  zai jagoranci wata tawaga ta mutane takwas da za su halarci bikin rufe wasannin na Olympics duk kuwa da cewar Koriya ta Kudu ta dade tana zargin Janar Kim Yong Chol da hannu cikin kai hare-hare a fadin kasar,

A daya bangaren gwamnatin Koriya ta Kudu ta bakin kakakin hukumar hadin kan kasar Baek Tae-hyun ta bayyana cewar tana sane da irin kallon da mutanen kasar suke wa Janar Kim duk kuwa da cewar kasar na fata bisa dorewar ingantuwar alaka tsakanin kasashen na Koriya.