Wasu ƙarin jama′ar sun kamu da Ebola | Labarai | DW | 13.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu ƙarin jama'ar sun kamu da Ebola

Ƙungiyar lafiya ta duniya WHO ta ce an samu ƙarin wasu sabbin mutane 128 da suka ka kamu da cutar Ebola a yammacin Afirka.

Sanarwar ta ƙungiyar ta ce mutane 56 suka mutu da cutar a cikin kwanaki biyun da suka wuce a yammancin Afirka.

Hukumar ta ce tun daga lokacin da anobar ta ɓarke a cikin watan Maris, kawo yanzu ta kashe mutane 1069 yayin da aka tabbatar da cewar wasu 1975 sun kamu da cutar. Sama da mutane dubu ɗaya suka mutu da cutar a cikin ƙasashen Liberia da Gini da Saliyio da kuma Najeriya yazuwa yanzu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo