1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar cin kofin kwallon fata ta duniya

Suleiman Babayo
April 4, 2022

Sharhin raba kasashe 32 a rukunoni na wasan neman cin kofin kwallon kafa ta duniya da kasaa Katar za ta dauki nauyi cikin wannan shekarar ta 2022.

https://p.dw.com/p/49Rxb
Katar | Taron FIFA a Doha | Gianni Infantino
Hoto: Franck Fife/AFP/Getty Images

Kasar Jamus ta fada rukunin E inda kasashen Spain da New Zealand da Japan suka fada. Sannan Faransa mai rike da kambun wasan tana rukunin D da ya kunshin kasashen Faransa da United Arab Emirates da Australia da Peru da Denmark da kuma Tunisia.

Katar | Babban taron FIFA a Doha
Hoto: Franck Fife/AFP/Getty Images

A wasannin lig na Jamus wato Bundesliga, Union Berlin ta doke FC Kolon 1 da nema, Arminia ta tashi 1 da 1 da kungiyar Stuttgart, sannan Leverkusen ta doke Hertha Berlin 2 da 1, a nata bangaren Frankfurt ta tashi babu wadda ta jefa kwallo a raga yayin wasa da kungiyar Greuther Fürth kana Augsburg ta doke Wolfsgsburg 3 da nema, ita kuma kugiyar Bochum ta bi Hoffenheim gida ta doke ta 2 da 1.

Katar Doha | Jamus na rukunin E
Hoto: HAMAD I MOHAMMED/REUTERS

Sannan kungiyar Bayern Munich ta bi Freiburg har gida ta lallasa ta 4 da 1, kuma wannan wasa muka gabatar kai tsaye daga nan sashen Hausa na DW wanda AbdulRaheem Hassan da Abdourahaman Hassane suka gabatar:

A wasannin lig na Ingila, Premier Lig, Manshester United ta tashi 1 da 1 da kungiyar Leicester, sannan Manchester City ta bi Burnley har gida ta doke ta 2 da nema, a nata bangaren kungiyar West Ham ta doke Everton 2 da 1.

Karawar Barcelona da Real Madrid Cristiano Ronaldo da Daniel Alves
Hoto: dapd

A wasannin La Liga na Spain, Real Madrid ta bi Celta gida ta lallasa ta 2 da 1, kana Barcelona ta doke Sevilla 1 mai ban haushi. Ita kuma Betis ta yi raga-raga da Osasuna 4 da 1.

Babban jami'in hukumar kula da wasan zari-ruga na duniya, Alan Gilpin ya ce kasar Australiya tana bukatar 'yan wasa masu kuzari lokacin wasan duniya na maza na shekara ta 2027 da na mata ta shekarar 2029, kuma babban jami'in ya fada haka lokacin da Australiya ta gabatar da neman daukar nauyin wasan na mata na shekara ta 2029.