Warware saɓani tsakanin Hamas da Fatah | Labarai | DW | 19.11.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Warware saɓani tsakanin Hamas da Fatah

Musayar harbe-harbe a tsakanin Isra'ila da zirin Gaza ta tilastawa Hamas da Fatah dunƙulewa wuri guda.

A yayin da Isra'ila ke ci gaba da ƙaddamar da hare-hare ta jiragen sama akan zirin Gaza na Falasɗinu, kuma take fuskantar martanin rokoki, ƙungiyoyin Hamas da Fatah na Falasɗinawa, waɗanda ba sa ga maciji da juna sun bayyana dunƙulewa wuri guda domin nuna goyon bayan su ga zirin na Gaza.

Wani jigo a ƙungiyar Fatah Jibril Rajoub, ya shaidawa wani taron masu zanga-zangar da yawan su yakai mutane dubu ɗaya a yankin gaɓar tekun Jordan, da ke zama hedikwatar Falasɗinu cewar, daga wannan lokacin, yana tabbatarwa da duniya cewar sun kawo ƙarshen taƙaddamar da ke tsakanin su. Daga ciki waɗanda suka halarci taron na yankin gaɓar tekun Jordan - harda shugabannin ƙungiyar Hamas a yankin da kuma na ƙungiyar Islamic Jihad.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Isra'ila ta shiga yini na shidda a jere wajen farmakin da take ƙaddamarwa a Gaza, wanda ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas, kana 'yan ƙungiyar ta Hamas kuwa ke jefa rokoki a cikin Isara'ila.

A halin da ake ciki kuma, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta bayyana yiwuwar tsagaita buɗe wuta a rikicin na zirin Gaza, yayin da ministan kula da harkokin wajen na Jamus Guido Westerwelle ya kama hanyarsa ta zuwa birnin Tel Aviv na Isra'ila. A cewar Steffen Seibert, kakakin shugabar gwamnatin Jamus, Merkel na fargabar yiwuwar rikicin na Gaza, ya tsananta rigingimun da dama yankin na Gabas Ta Tsakiya ke fama da shi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal

 • Kwanan wata 19.11.2012
 • Muhimman kalmomi Gaza
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16leN
 • Kwanan wata 19.11.2012
 • Muhimman kalmomi Gaza
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16leN