1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Warware rikicin shiga majalisar dokokin Turai

February 26, 2014

Kotun Kolin Jamus ta sahhalewa kananan jam'iyun kasar shiga majalisar dokokin Turai.

https://p.dw.com/p/1BFdv
Bundesverfassungsgericht Karlsruhe EFSF Sondergremium
Hoto: Reuters

Kotun kolin tarayyar Jamus ta zartar da hukuncin soke sharadin cewar, jam'iyyun siyasar kasar na bukatar samun akalla kaso uku cikin 100 na kuri'u gabannin samun damar shiga majalisar dokokin Kungiyar Tarayar Turai, a wani abin da ke zama bude kofar samun karin jam'iyyun da za su yi nasarar samun kujeru a zaben da zai gudana cikin watan Mayu - idan Allah ya kaimu. A dai bara ne gwamnatin Jamus ta rage yawan kason da ya kamata jam'iyun su samu daga biyar cikin 100 zuwa uku cikin 100, amma a wannan Larabar (26. 02. 14), kotun kolin ta ce hakan ya sabawa tsarin mulkin kasar, inda ma ta soke baki daya tarnakin da kananan jam'iyun ke samu wajen cimma burinsu, tana mai cewa kayyade kuri'un ya sabawa 'yancin daidaiton da jam'iyun siyasa ke dashi. Dama gungun wasu kananan jam'iyu ne suka garzaya zuwa kotun, inda suka bukaci ta yi bitar ka'idar kaso uku cikin 100, wanda suka ce ba adalci a ciki, kuma take hakkin wasu magoya bayan jam'iyun ne. Biyar daga cikin alkalai takwas da suka saurari shari'ar ne suka yi na'am da bukatar kananan jam'iyun, inda suka kafa hujjar cewar, tilas ne kowane mai jefa kuri'a ya samu daidaiton 'yancin tantance wakilan da za su shiga majalisar dokokin tarayyar Turai.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar