Warkaswa ta hanyar sautin kida a kasar Ghana | Himma dai Matasa | DW | 24.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Warkaswa ta hanyar sautin kida a kasar Ghana

Muhammamad Alidu yana rera waka ne tare da sautin da ke warkas da marasa lafiya a irin sautikan da ya tsinto daga tatsuniyoyin mutanen da, kuma ya hada da tsofaffin wakoki.

Kasancewar Alidu masani ne a fannin kida da waka ya gina makaranta don koya wa yara kida da waka a garin Tamale da koya musu yin amfani da sauti domin samar da zaman lafiya a tsakanin al'umma, makarantar ta shi tana da dalibai sama da 150. Sai dai ya ce babbar matsalar da yake fuskanta ita ce ta addini, domin iyayen yara Musulmi basa barin 'ya'yansu suje makarantarsa saboda sun ce addinin Musulunci bai amince da wannan kida ba.

Hanan Abdul Halik daya ne daga cikin makadan a lokacin da yake dukan wani katako da aka hada a matsayin garaya,yana gwaji ne kafin wani wasa da za su yi a wata makarantar koyon sauti mai suna Bizung daura da Norrrip a garin Tamale. Wannan irin tsohuwar waka daga daliban makarantar sautin, yana kara wa 'yan mata karsashi wajen 'yan matanci, Muhammad Alidu mai yin magani da sauti shi ne wanda ya kirkiri makarantar Bizung ta koyon sauti kuma mataimakansa a harkar sun bada amannar cewa akwai irin kidan da yake magani ga marasa lafiya.A halin yanzu Alidu mai magani da sauti yana zagayawa a cikin kasar Ghana don yin magani ga masu lalurar damuwa, inda yakan yin wasan sa kai tsaye a bainar jama'a, kuma babban burin Alidu bai wuce ganin ya inganta koyon sauti a arewacin kasar ba. shiya sa ma makarantun da ya kirkira don koyar da irin wannan sauti na shi kyauta ne. Bangaren Arewa shi ne inda Musulmi suka fi yawa.

Iyaye da yawa sun ce addinin Musulinci bai amince da salon irin wannan kida da waka ba shiya sa suka cire 'ya'yansu daga irin wadannan makarantu. Wani Malamin addini Malam Habib Hussein Baba Tamale ya ce akwai mawakan da idan ka saurari irin sakon da ke cikin wakokin su, babu komai a ciki sai batsa da koyar da miyagun dabi'u, wannan ta sa addinin Musulinci bai amince da irin wannan koyarwa ba.