Wariyar launin fata ga bakar fata a Maroko | Siyasa | DW | 21.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wariyar launin fata ga bakar fata a Maroko

An hana yin magana game da wariyar launin fata a Maroko. An kuma boye batun bakar fatan kasar dalilin haka ya sa ba a iya magana game da irin matsalolinsu na wariya wannan shi ne batun da shirin Taba Ka Lashe ya duba.

Saad Bouh Rabah shugaban wata kungiyar da ke yaki da nuna wariyar launin fata a kudancin Maroko

Saad Bouh Rabah shugaban wata kungiyar da ke yaki da nuna wariyar launin fata a kudancin Maroko

A dangane da jerin zanga-zangar da muhawara kan wariyar launin fata a Amirka, kasashe da dama cikin har da na Afirka na duba munin matsalar a cikin gida. A Maroko da ke arewacin Afirka har yanzu ba a ji komai ba dangane da wannan batu duk da wariya da kuma kyama da ake nuna wa bakar fatar wannan kasa. Domin tun gabanin zuwan Turawan 'yan mulkin mallaka, Larabawa ne suka mamaye yankin inda masanan tarihi suka ce tun a wancan zamani ne aka assasa harsashin wariyar launin fata. Sau tari dai duk wanda ke magana game da wariyar launin fata a Maroko ya kan ji babu dadi a gun jama'a. Su ma baki  'yan ci-rani na zargin karuwar matalsar wariyar launin fata a Maroko. 

Rayuwar bakar fata da ake maida su tamkar baki a kasarsu ta asali

Gnawa da Haratin na zama wasu bangarori na al'umar bakar fatar Maroko da bisa tarihi ke rayuwa a yankin kudancin kasar. Har yau ana yawaita jin wakoki da kade-kaden wadannan al'umomin a bukukuwa kamar na aure da dai sauransu. Salon kade-kaden wadannan al'umomin bakar fatar na Maroko sun shahara a fadin duniya. An yi kiyasin cewa kashi 10 cikin 100 na al'umar Maroko, bakar fata ne da suka yi kaura daga kasashen Afirka kudu da Sahara. Sai dai duk da haka bakaken fatan a Maroko ba a yawaita ganinsu a bainar jama'a a cewa M'barek Bouhchichi, wanda bakar fata ne kuma dan fasaha daga birnin Akka na kudancin Maroko a kusa da iyakar kasar da Aljeriya. Da shi da takwarorinsa masu fasaha sun wallafa wani littafi kan rayuwar bakar fata da ake maida su tamkar baki a kasarsu ta asali. "Idan a yau ka nemi wani ya kwatanta maka yadda Maroko take ko ya yi maka bayanin yanayin zamantakewa a kasar, ba zai taba cewa tana da yawan bakaken fata ba. Zan iya cewa an riga an cusa mana ra'ayin yin watsi da asalinmu na 'yan Afirka."

Raba makabartun farar fata da na bakar fata dabam-dabam a kudancin Maroko

Masanin ya ce an haramta yin magana game da wariya da kuma tarihi na bauta a kasar. An kuma boye batun bakar fatan kasar dalilin haka ya sa ba a iya magana game da matsalolinsu. Masanin ya ce wannan matsala ta wariya ta zama ruwan dare a fadin kasar. Wani bincike ma da ya yi ya gano cewa a kudancin kasar an raba makabartun bakar fata dabam na farar fatan 'yan Maroko kuma dabam.

 

Sauti da bidiyo akan labarin